Tsaro
Kaduna: Ƴan sun tabbatar da sace ɗaliban Saint Albert College
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ta tabbatar da rahoton kai hari kwalejin Saint Albert, da ke yankin ƙaramar hukumar Jama’a
Mai magana da yawun rundunar ASP Muhammad Jalige, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Talatar makon nan.
Sanarwar ta ce ƴan bindiga sun kai hari kwalejin ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Haka kuma Muhammad Jalige ya ƙara da cewa, yayin harin, ƴan bindigar sun sun yita yin harbe-harbe kana daga bisani suka sace dalibai 3.
Sanarwar ta kuma yaba wa al’umma bisa irin bayanan sirri da suke bai wa jami’an tsaro.
