Connect with us

Featured

Dangote ya bayyana shirin zuba jarin dala biliyan 70 a Afirka, domin tabbatar da Afirka ta tsaya da ƙafafuwanta  

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfaninsa na shirin ƙara jarin da yake zubawa a nahiyar Afirka daga dala biliyan 50 zuwa biliyan 70 nan da shekarar 2030, tare da faɗaɗa harkokin samar da wutar lantarki domin ƙarfafa masana’antu da bunƙasa tattalin arzikin nahiyar.

Dangote ya bayyana waɗannan tsare-tsare ne yayin wata ganawa da ’yan jarida, masu rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta (Bloggers), masu ƙirƙirar abubuwan wallafawa (Content Creators), masu shirya fina-finai da sauran masu ruwa da tsaki daga Arewacin Najeriya, waɗanda suka kai rangadin ziyara matatar man fetur ta Dangote da masana’antar taki da sinadarai da ke Lekki, jihar Legas, ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026. A yayin tattaunawar, ya kuma yi bayani kan tafiyar da ya yi daga harkar saye da sayarwa zuwa kafa manyan masana’antun ƙera kayayyaki.

Daya daga cikin manyan tsare-tsaren da ya bayyana shi ne shirin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 10,000 a faɗin Afirka, ciki har da yiwuwar aiwatar da shi a Najeriya. Ya ce a halin yanzu kamfanonin rukunin Dangote na iya samarwa da kansu wutar lantarki kusan megawatt 1,500, yayin da ake sa ran ƙarfin zai kai tsakanin megawatt 4,500 zuwa 5,000 kafin kammala shirin Vision 2030. Ya bayyana cewa ƙarancin wutar lantarki na ci gaba da zama babban cikas ga ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa, musamman waɗanda ke kashe kuɗaɗe wajen amfani da janaretocin mai da dizal, don haka ya buƙaci gwamnati ta samar da manufofi da yanayin da zai ƙarfafa zuba jari da samar da ayyukan yi.

Baya ga batun masana’antu da makamashi, Dangote ya yi kira da a mayar da hankali wajen sarrafa albarkatun gona da ma’adinai a cikin gida, maimakon fitar da su zuwa ƙasashen waje a matsayin ɗanyen kaya. A cewarsa, sarrafa irin waɗannan albarkatu a cikin gida zai taimaka wajen ƙara musu daraja, samar da damammakin ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

Da yake bayyana abin da ya taimaka masa wajen gina nasarar kasuwancinsa, Dangote ya ce sirrin shi ne jajircewa, dagewa da kuma mayar da hankali wajen cimma manufofin da mutum ya sanya a gaba. Ya bayyana cewa komawarsa Legas a shekarar 1978 ya zo da ƙalubalen sabawa da sabon yanayin rayuwa, musamman saboda bambancin al’adu da salon rayuwa da wanda ya saba da shi a Arewa. Sai dai ya ce bai bari waɗannan matsaloli su kawar da hankalinsa daga burinsa ba, inda ya ci gaba da jajircewa har ya samu nasarar da ake gani a yau.

Dangote ya bayyana cewa gina kasuwanci mai ɗorewa na buƙatar ladabi da bin ƙa’idoji, yana mai jan hankalin ‘yan kasuwa da su guji kashe kuɗin da ba su samu ba tukuna. Ya kuma bayyana cewa ba kowane irin kasuwanci ne yake samun nasara ba, don haka dole ne ɗan kasuwa ya kasance mai lura da yadda harkokinsa ke tafiya, tare da fahimtar lokacin da ya dace ya janye daga kasuwancin da ba ya kawo sakamakon da ake fata.

Ya ƙara da cewa idan ɗan kasuwa ya fahimci cewa lissafin harkarsa ba ya tafiya yadda ya kamata, bai kamata ya nace a kanta kawai saboda ya riga ya saka jari ba. A maimakon haka, ya kamata ya kasance da ƙarfin hali na sauya hanya ko dabarun gudanar da kasuwancin domin kauce wa asara da samar da damar samun ci gaba. Wannan na daga cikin darussan da ya ce suka taimaka wajen tafiyarsa daga ƙaramin kasuwanci zuwa manyan masana’antun da yake gudanarwa a yau.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet