Addini
Tinubu zai tafi Umara domin yi wa Najeriya addu’a
A ranar Alhamis 29 ga Oktoba, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja zuwa birnin Makka na ƙasar Saudiyya, domin gudanar da ibadar Umrah.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Read Also : Kotu ta umarci INEC ta cire sunan Uzodinma tare da sanya Rochas a matsayin ɗan takarar Sanatan Imo ta Yamma
Onanuga ya ce ziyarar za ta bai wa Tinubu damar yin ibada, tare da yin addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaban Najeriya.
Kafin tafiyar tasa, ana sa ran shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da rundunar sojin sama ta Najeriya ta saya a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, sannan ya dawo Najeriya a mako mai zuwa.

Pingback: Tinubu zai gabatar da kasafin 2027 kafin ƙarshen shekara - KAKAKI 24