Featured
Kano : Kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da shaye-shaye da fadan daba ya kama ‘Malam Keya’ bisa zargin jagorantar kungiyoyin ƴan daba a Dala
Kwamitin yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi na Jihar Kano ya kama Ishaq Lawan Ibrahim, wanda aka fi sani da “Malam Keya”, a birnin Port Harcourt na Jihar Rivers.
Shugaban kwamitin, Muhuyi Magaji, ya bayyana hakan ranar Alhamis, inda ya ce an dawo da wanda ake zargin zuwa Kano domin fuskantar shari’a.
Read Also : NCC Ta Ƙaddamar Da Manhajar Tantance Wayoyi a Najeriya
Muhyi ya ce ana zargin Malam Keya, mai shekaru 27, da jagorantar tare da ɗaukar nauyin rikice-rikicen ’yan daba da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a Ƙaramar Hukumar Dala da wasu sassan Kano.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya tsere daga Kano ne bayan ƙara tsaurara matakan tsaro, amma jami’an kwamitin sun bi sahunsa ta hanyar bayanan sirri har suka kama shi a Port Harcourt. Magaji ya kuma yaba wa rundunonin ’yan sandan Kano da Rivers bisa taimakon da suka bayar wajen gudanar da samamen.

Pingback: Har yanzu INEC ba ta tabbatar da takarar Gwarzo ba - KAKAKI 24