Featured
Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Wutar Lantarki Ta Sa’o’i 24 a Kano, Legas Da Wasu Birane – Ministan Lantarki
Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin kafa wasu yankunan makamashi na musamman, wato Energy Zones, domin samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24 a manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu.
An bayyana hakan ne bayan wata ganawa tsakanin Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, da shugabannin wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki a Abuja. Shirin zai mayar da hankali kan yankunan Legas, Abuja-Kaduna-Kano, Enugu da Port Harcourt.
Read Also : Gwamnatin Tarayya Ta Bayar da Hutu Domin Bikin Ranar ’Yancin Kai
Ministan ya ce matsalar wutar lantarki a Najeriya ba ta tsaya kan yawan wutar da ake samarwa ko hanyoyin isar da ita ba, domin akwai kuma ƙalubalen karɓa da rarraba wutar ga masu amfani. Ya ce Energy Zones za su taimaka wajen rage wannan gibi.
Ya ƙara da cewa shirin zai ƙarfafa hanyoyin karɓar kuɗaɗen wutar lantarki daga kamfanonin rarrabawa tare da ƙara gine-ginen ababen more rayuwa a wuraren da ake da yawan buƙata, domin tallafa wa masana’antu, samar da ayyukan yi da bunƙasa harkokin kasuwanci.

Pingback: Nigerian Democracy Working Group Urges Restraint Over Reported Kano Rally - KAKAKI 24