Connect with us

Featured

Duk kansilan da ya ciyo wa Tinubu zaɓe a mazaɓarsa, za mu bashi kyautar Naira Miliyan 10 – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga duk wani kansila da ya tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a mazabarsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, sarakunan gargajiya da mazauna ƙaramar hukumar Kwali da ke Abuja. Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa goyon bayan al’umma ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Ministan ya kuma yi kira ga kansiloli da shugabannin ƙananan hukumomi da su haɗa kai wajen wayar da kan matasa, mata da sauran al’umma domin samun nasarar Tinubu. Ya kuma bayyana shirinsa na shirya wani taron musamman domin ƙarfafa gangamin siyasar.

Baya ga batun zaɓen 2027, Wike ya nemi a ƙara wa mazauna Abuja damar wakilci a majalisar dokokin ƙasa, yana mai cewa yawan jama’ar yankin bai dace da ƙarancin wakilcin da suke da shi ba. Haka kuma, ya yi alƙawarin duba matsalar bambancin albashi tsakanin kansiloli da kuma tabbatar da kammala ayyukan tituna da gadoji a ƙananan hukumomin Abuja.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet