Connect with us

Featured

Gwamnatin Sokoto Ta Musanta Zargin Bai Wa Ƴar TikTok Kyautar Mota

Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin gwamna Ahmed Aliyu ta musanta labaran da ke yawo cewa gwamnan na da hannu wajen bai wa wata ƴar TikTok kyautar mota. Gwamnatin ta ce babu wata alaƙa tsakanin gwamnan da batun bayar da motar.

A cikin wata sanarwa da daraktan harkokin yaɗa labaran gwamnan jihar, Abubakar Bawa ya fitar, ya bayyana cewa ofishinsa na tsame Gwamna Ahmed Aliyu gaba ɗaya daga batun. Ya ce kyautar ba ta da alaƙa da gwamnan ta kowace fuska.

Lamarin ya biyo bayan wani bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta a ƙarshen mako, inda aka ga wasu maza biyu suna miƙa mota ga wata sananniyar ƴar TikTok a Sokoto. Mutanen sun ce sun ba ta motar ne bisa “soyayyar” da take yi wa gwamnan, abin da ya janyo suka da zargin an yi amfani da kuɗin gwamnati.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet