Addini
Ba mu hana ɗalibai mata masu niƙabi shiga makaranta ba – Kwalejin Shari’a ta Aminu Kano
Mahukuntan Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Koyon Shari’a ta Aminu Kano (AKCILS) sun musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa suna hana ɗalibai mata masu sanya niƙabi shiga harabar makarantar.
A cikin wata sanarwa, kwalejin ta ce zargin ba gaskiya ba ne, tana mai cewa ana gudanar da binciken tsaro ne ga dukkan ɗalibai da ma’aikata domin hana shigar da abubuwan da za su iya zama barazana ga tsaro.
Read Also : Amurka ta ci amanarmu – Shugaban Ukraine
Mahukuntan sun bayyana cewa ana buƙatar ɗalibai masu niƙabi su bayyana fuskokinsu kawai a wurin binciken domin tantance su, tare da bincikar jakunkunansu. Sun jaddada cewa ba a tilasta musu cire niƙabi ko cin zarafinsu, kuma ba a taɓa hana wata ɗaliba ko ma’aikaciya shiga saboda sanya hijabi ko niƙabi ba.
Kwalejin ta zargi masu yaɗa jita-jitar da yin hakan domin biyan muradunsu na kashin kai da haddasa ruɗani. Ta kuma tuna da wani lamari na shekarar 2014, lokacin da jami’an tsaronta suka hana wata mata da ake zargi shiga makarantar, wadda daga baya ta tayar da bam a ƙofar Kano State Polytechnic.

Pingback: Gwamnatin Zamfara Za Ta Siya Wa Mutane 36,176 Hannayen Jari a Kamfanin Dangote - KAKAKI 24