Featured
Atiku Ya Buƙaci Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Inda N10bn Da Aka Ware Domin Tunkarar Cutar Ebola Suke
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi wa ’yan Najeriya bayani kan inda Naira biliyan 10 da aka ware domin shirin tunkarar cutar Ebola suke.
A ranar 9 ga Yuni ne Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin Naira biliyan 10 domin shirye-shiryen gaggawa kan Ebola.
Read Also : Tinubu ya cancanci yin wa’adi na biyu a kujerar shugabancin Najeriya – Abdulaziz Abdulaziz
A wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar a madadin Atiku, ya ce dole a yi cikakken bayani kan kudin, musamman bayan tabbatar da wani mai ɗauke da Ebola a Abuja.
Atiku ya kuma tambayi gwamnati lokacin da aka fara zargin cutar, lokacin da hukumomin lafiya suka samu sanarwa, da kuma lokacin da aka fara bin diddigin mutanen da suka yi hulɗa da majinyacin.
