Featured
INEC Za Ta Bayyana Matsayarta Kan Rikicin ADC a Mako Mai Zuwa
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta duba rikicin shugabancin jam’iyyar ADC a wani taronta da ake sa ran gudanarwa a mako mai zuwa, bayan dawowar shugabanta daga tafiya.
Kwamishinan hukumar kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mallam Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan. Ya ce har zuwa daren Talata hukumar ba ta samu kwafin hukuncin kotu da aka tabbatar da sahihancinsa ba, duk da cewa ta karɓi ƙarar ɗaukaka kara da neman dakatar da aiwatar da hukuncin daga ADC.
Read Also : PDP Ta Yi Alla-Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Magoya Bayan Pantami a Gombe
A wani rahoto makamancin haka, wasu ‘yan takarar ADC da mambobin ƙungiyar United Friends for Atiku (UFFA) sun shigar da ƙorafi ga ofishin jakadancin Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya, bisa zargin nuna son kai a ɓangaren shari’a. Ƙungiyar ta kuma zargi jinkirin fitar da kwafin hukuncin kotun da ya soke kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.
Shugaban ƙungiyar, Audu Aliyu, ya ce sun ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke ranar 5 ga Nuwamba, tare da bayyana cewa sun bi hanyoyin doka wajen neman haƙƙinsu. Ya ce sun aika da ƙorafin ga Shugaba Bola Tinubu, NJC, NBA, Kotun Ɗaukaka Ƙara, ECOWAS, Majalisar Ɗinkin Duniya, Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka.

Pingback: Mataimakin Sakataren Yaɗa Labaran NDC Na Ƙasa Ya Fice Daga Jam’iyyar - KAKAKI 24