Connect with us

Featured

Da ɗumi ɗumi : Kotu ta soke shugabancin David Mark, tare da soke takarar Atiku Abubakar

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke dukkan matakan da shugabancin ya ɗauka a madadin jam’iyyar, ciki har da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.

A hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke ranar Alhamis, kotun ta bayyana kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark a matsayin wanda ya saɓa wa doka. Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana ƙalubalantar yadda kwamitin ya karɓi shugabancin ADC.

Nafiu Bala Gombe ya yi ikirarin cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci karɓar ragamar shugabancin. Ya kuma nemi kotu ta hana David Mark da Rauf Aregbesola gabatar da kansu a matsayin shugaban jam’iyyar da sakatarenta, bisa hujjar cewa naɗinsu ya saɓa wa kundin tsarin jam’iyyar da dokar zaɓe.

Sai dai jam’iyyar ADC ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara. Hukuncin ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan Atiku ya gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓensa a jihar Sakkwato, yayin da tuni INEC ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takara, kuma ya zaɓi tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakinsa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet