Connect with us

Featured

NEDC Na Tattaunawa Da Masu Ruwa Da Tsaki Bisa Shirin Rarraba Motocin Lantarki A Yobe

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Hukumar raya yankin arewa maso gabas ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Damaturu gabanin shirin gwamnatin tarayya na tura motocin lantarki guda 10,000 a fadin yankin arewa maso gabas.

Shirin, wanda aka jagoranta karkashin Ajandar fata mai dorewa, yana da nufin samar da hanyoyin sulfuric na jama’a masu rahusa da kuma hanzarta farfadowar tattalin arziki a yankin.

Hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) ta fara taron masu ruwa da tsaki a Damaturu, gabanin shirin gwamnatin tarayya na rarraba motocin lantarki (EVs) guda 10,000 a fadin yankin.

Kamar yadda rahoton ya ke cewa shiga tsakani, wanda gwamnatin tarayya ta fara karkashin shirin ajandar fata mai dorewa, na da nufin samar da sufuri mai rahusa da kuma bunkasa farfaxowar tattalin arziki.

Babura masu tayoyi uku ne guda 10,000 yayin da motoci taksi guda 300 hade da motocin bas guda 30 na daga cikin abubuwan hawan da aka ware masu amfani da ka lantarki da za’a rarraba su ga yankunan na arewa maso gabas don saukaka wa al’umma wahalhalun sufuri.

Da yake jawabi a wurin taron, Kodineta na hukumar ta NEDC a jihar ta Yobe, Farfesa Ali Abbas, ya ce daraktan hukumar, Dr Mohammed Alkali, na inganta zirga-zirgar ababen hawa na yanayi da kuma tattalin arziki dai-dai da ajandar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce manufar tattaunawar ita ce, a samo ra’ayoyi daga muhimman masu ruwa da tsaki a bangaren sufuri na jihar domin aiwatar da aikin yadda ya kamata.

Abbas ya ce masu ruwa da tsakin da suka hada da ma’aikatar Sufuri, ‘yan sanda, hukumar kula da kare hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar direbobin sufuri ta kasa (NURTW), sarakunan gargajiya da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) na daga cikin waɗanda suka halarta.

A cewarsa, motocin lantarki sun fi rahusa wajen kulawa kuma ba sa gurbata muhalli idan aka kwatanta su da motocin gargajiya masu amfani da makamashin man fetur da dizel.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa shirin rarraba motocin lantarkin zai rage tsadar sufuri da ya biyo bayan cire tallafin man fetur.

Kodineta ya sanar da cewa shirin ya kai matakin karshe na kafa tashoshin cajin motocin lantarki a jihohi shida na yankin.

A nasa jawabin, Kwamishinan sufuri da makamashi, Alhaji Muhammed Bara, ya ce baburan masu kafa uku na lantarki za su karfafawa matasa gwiwa ta hanyar samar da ayyukan yi.

Baburan za su karfafa tattalin arzikin matakin qasa, samar da hanyoyin sadarwa masu rahusa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.

Motocin taksi 300 za su zamanantar da tafiye-tafiyen cikin gari, tare da ba da rahusa ga matafiya.

Haka kuma su motocin bas xin za su zama kashin bayan sufurin jama’a da ke hada garuruwanmu, tare da rage nauyi a kan hanyoyinmu, inji shi.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet