Featured
NiMet Ta Yi Hasashen Samun Zafin Rana Mai Tsanani a Arewacin Najeriya
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, Nigerian Meteorological Agency, ta yi gargaɗin yiwuwar samun matsanancin zafi a wasu sassan ƙasar, wanda zai iya jefa mutane cikin galabaita. Ta ce jihohin arewa kamar Neja, Kebbi, Kano, Sokoto, Zamfara, Katsina, Yobe, Jigawa, Bauchi, Gombe, Borno da Adamawa ne za su fi fuskantar lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa yanayin zafin na iya kaiwa tsakanin maki 40 zuwa 45 a arewacin ƙasar, yayin da a tsakiyar ƙasar zai kai maki 35 zuwa 38, a kudanci kuma zai kasance tsakanin maki 33 zuwa 35. Ta kuma ce akwai yiwuwar wasu jihohin da ba a ambata ba su fuskanci ƙarin zafi.
Hukumar ta buƙaci al’umma su riƙa shan ruwa sosai, su zauna a wurare masu iska, su guji cunkoso da yawan zama a ƙarƙashin rana. Haka kuma ta shawarce su da su sanya hula da gilashi idan za su fita, tare da amfani da kayan da ba su da nauyi.
