Featured
Kotun Koli Ta Sanya Ranar Ci Gaba da Shari’ar Masarautar Kano a 2027
Kotun kolin Najeriya ta ayyana ranar 19 ga watan Afrilu, 2027 domin ci gaba da sauraron shari’ar masarautar Kano. An tsayar da ranar ne domin saurare da kuma karɓar martanin waɗanda aka shigar da ƙara a kansu.
Shari’ar dai ta samo asali ne daga ƙarar da Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar, inda yake ƙalubalantar wasu matakai da aka ɗauka dangane da dokokin masarautar. Kotun na shirin sauraron ɓangarorin biyu domin tantance hujjojin da aka gabatar.
Mai ƙarar na zargin an tauye masa haƙƙinsa na doka a matsayin babban ɗan majalisar sarki, sakamakon sauyin dokar masarautu da majalisar dokokin Kano ta yi.
