Connect with us

Featured

Rikicin Masarautar Kano: Yadda Ta Wakana a Zaman Babbar Kotun Jihar Kano

Babbar kotun jihar Kano ta dage zaman sauraron karar da gwamnatin Kano ta shigar na neman dakatar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan da aka cire daga ayyana kansu a matsayin Sarkuna zuwa 2 ga watan Yuli na 2024.

Mai shari’a, Amina Adamu Aliyu ce ta dage zaman bayan sauraron muhawarar kowanne bangare.

Lauyan Aminu Ado Bayero, Barista Ibrahim Mukhtar da Lauyan Gwamnati, Barista Ibrahim Isah-Wangida duka sun gabatar da bayanan kararsu a gaban kotun.

A zaman na yau, Lauya Abdulrazak Ahmad ya tabbatar da cewa an sada Aminu Ado da bayanan karar inda ya nemi kotun ta kori karar inda ya ya bayyana cewa bata da hurumi.

Sai dai lauyan Gwmanati, Barista Ibrahim Isah-Wangida ya ce kotun tana da hurumi inda ya bukaci ta saurari karar.

Daga nan ne mai shari’a Amina Aliyu ta dage sauraron karar zuwa 2 ga watan Yuli domin duba bukatar kowanne bangare tare da ci gaba da sauraron karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar gabanta.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet