Featured
Sarkin Kano ya yi Alla-wadai da lalata fastocin Gwamnan Kano, tare da umartar gaggauta gyara su
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nuna rashin jin dadinsa kan lalata fastocin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da wasu magoya bayansa suka yi, tare da bayar da umarnin a gaggauta gyara wadanda aka lalata.
Babban Mashawarcin Sarkin, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, kuma Sarkin Dawaki Babba, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce Sarkin ya jaddada cewa, masarautar gargajiya sama take da jamiyyun siyasa, domin a cewarsa, su iyayen al’umma ne ba ƴan siyasa ba.
Read Also : Ina cikin ƙoshin lafiya kuma a shirye nake na cigaba da aiki gadan-gadan – Tinubu
Sarkin Dawaki Babba ya kuma bayyana godiyar Sarkin ga dubban magoya bayansa, maza da mata, matasa da dattawa, wadanda suka raka shi a kafa zuwa fadarsa da ke Nassarawa, duk da ruwan sama mai karfi da iska.
Ya ce Sarkin ya bukaci magoya bayansa da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Jihar Kano da Najeriya, tare da rokon Allah Ya albarkaci al’ummar kasar baki daya.

Pingback: Gwamnatin Tarayya Ta Bayar da hutu Domin Bikin Ranar ’Yancin Kai - KAKAKI 24