Featured
Malaysia Ta Haramtawa Yara Ƴan Ƙasa da Shekaru 16 Amfani da Shafukan Sada Zumunta
Ƙasar Malaysia ta fara aiwatar da dokar hana yara masu ƙasa da shekara 16 buɗe ko amfani da shafukan sada zumunta a faɗin ƙasar.
Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Malaysia ta bayyana cewa dole ne shafuka irin su Facebook da Instagram da TikTok da YouTube su riƙa tantance shekarun masu amfani da su ta hanyar bayanan gwamnati da aka amince da su.
Matakin ya zo ne yayin da Malaysia ta bi sahun wasu ƙasashe da suka ɗauki irin wannan tsari domin kare yara daga kallon abubuwan da ba su dace ba a shafukan sada zumunta. Kamfanonin da suka karya dokar na iya fuskantar tarar kusan dala miliyan 2.5.
