Featured
Bincike: Gwamnan Kano ya buƙaci a sauya masa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci a sauya kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, tare da jami’an ’yan sanda 18 masu kula da ofisoshin ’yan sanda (DPOs) a wasu sassan jihar, gabanin babban zaɓen 2027, a cewar wani rahoton jaridar Daily Nigerian.
Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa gwamnan ya gabatar da sunan CP Mohammed Yusuf Adamu domin maye gurbin Bakori, yayin da ake sa ran sabon kwamishinan zai fara aiki nan ba da jimawa ba. Rahoton ya danganta matakin da rashin jituwa tsakanin gwamnan da kwamishinan kan sauye-sauyen jami’an ’yan sanda.
Rahoton ya kuma ce Sufeto-Janar na ’yan sanda ya sauya wuraren aikin DPOs 18 daga Kano zuwa wasu jihohi, ciki har da Yobe, Gombe, Kebbi, Sakkwato, Zamfara da Katsina. Sai dai wata takardar rundunar mai kwanan wata 15 ga Oktoba, 2026, ta bayar da umarnin mayar da wasu jami’an zuwa tsoffin wuraren aikinsu tare da yin wasu sabbin naɗe-naɗe.
Lamarin dai ya haifar da tambayoyi kan yiwuwar katsalandan na siyasa a harkokin naɗe-naɗen jami’an tsaro. Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sanda, Anietie Iniedu, kan lamarin bai amsa ba, yayin da kakakin gwamnan, Mustapha Mohammed, ya ce bai da masaniya kan batun, don haka ba zai iya yin tsokaci a kai ba.

Pingback: Zaɓen 2027 : Atiku Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro Idan Ya Zama Shugaban Ƙasa - KAKAKI 24