Featured
Gwamnatin Kano ta kashe Naira Biliyan 26.5 wajen gyare-gyare a Gidan Gwamnati da tafiye-tafiye cikin watanni shida
Bayanan da jaridar PUNCH ta tattara daga rahotannin aiwatar da kasafin kuɗin jihohi sun nuna cewa Gwamnatin Jihar Kano ta kashe kusan Naira biliyan 26.5 wajen gudanar da Gidan Gwamnati, Ofishin Gwamna da kuma tafiye-tafiyen aiki a cikin watanni shida na farko na shekarar 2026.
Haka kuma, an kashe ƙarin Naira miliyan 626.95 kan tafiye-tafiye da sufuri, lamarin da ya kai jimillar kuɗin da aka kashe zuwa kusan Naira biliyan 26.50 cikin watanni shida.
Idan aka kwatanta da shekarar 2025, kuɗin da aka kashe kan Gidan Gwamnati da Ofishin Gwamna ya ragu daga Naira biliyan 28.84 zuwa Naira biliyan 25.87, wato raguwar Naira biliyan 2.98, kwatankwacin kashi 10.32 cikin 100.
Read Also : Tinubu Ya Fi Obasanjo, Yar’Adua Da Sauran Shugabannin Najeriya Aiki – APC
Rahoton ya bayyana cewa kuɗaɗen ba albashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ko wasu abubuwan da ya kashe na kansa ba ne, sai dai sun haɗa da kuɗaɗen gudanarwa, ma’aikata, gyare-gyare, tsaro, ayyukan hukuma da sauran harkokin tafiyar da bangaren zartarwa na jihar.
Binciken PUNCH ya kuma nuna cewa a jihohi 33 da aka samu bayanansu, an kashe jimillar Naira biliyan 512.10 kan gidajen gwamnati, ofisoshin gwamnoni da tafiye-tafiye a farkon watanni shida na shekarar 2026.
