Featured
Dangote Da Habasha Sun Kulla Yarjejeniyar Gina Bututun Man Fetur Na Dala Miliyan 600
Attajirin Afirka, Aliko Dangote, da gwamnatocin Habasha da Djibouti sun cimma yarjejeniyar gina bututun man fetur da rumbun ajiyarsa, a wani aiki da zai lakume dala miliyan 600.
Aikin zai kunshi gina bututun mai mai tsawon kilomita 120, wanda zai hada tashar jiragen ruwa ta Damerjog da ke Djibouti da cibiyar rarraba mai ta Dewele a Habasha. Haka kuma, za a gina rumbunan da za su iya daukar kusan lita miliyan 400 na man fetur.
Read Also : Atiku Ya Sanya El-Rufai a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa
Ana sa ran fara aikin cikin watanni 18. Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya ce bututun zai rage lokacin jigilar mai daga Djibouti zuwa Addis Ababa daga kwanaki biyar zuwa kwana daya.
A matakin farko, za a rika jigilar muhimman albarkatun man fetur da suka hada da man jirgin sama, dizal da fetur. Dangote ya ce aikin zai karfafa makamashi a Habasha tare da inganta tsarin samar da man fetur na kasar.

Pingback: 2027: Peter Obi Ya Yi Watsi Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen OK Movement - KAKAKI 24