Tsaro
Gwamnatin Zamfara ta buɗe wasu kasuwannin mako-mako
Gwamnatin jihar Zamfara, ta sanar da buɗe wasu kasuwannin mako-mako a jihar bayan rufe su na fiye da watanni biyu a wani yunƙuri na magance matsalolin ƴan bindiga da suka addabi jihar.
Batun buɗe kasuwannin na cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Ibrahim Dosara, ya fitar.
Ta cikin sanarwar, Dosara, ya ce, gwamnatin jihar ta yanke shawarar buɗe kasuwannin ne biyo bayan samun sauƙin da jihar ta yi a fannin matsalolin tsaro tare da yawan ƙorafe-ƙorafen al’ummar jihar.
Kasuwannin da gwamnatin ta amince da buɗewar sun ne: kasuwar Nasarawar Burkullu da kasuwar Gusau da ta Shinkafi da Kasuwar Daji da ta garin Dan Jibga amma banda kasuwannin dabbobi.
Haka kuma Gwamnatin ta sanya dokokin hana shiga kasuwannin da bindiga, kuma ta hana yin barazana ga wani da sunan wata ƙungiya ko hukuma da sauran wasu dokoki.
