Connect with us

Uncategorized

Na samu ɗaukakar da ko a mafarki ban yi tunanin samunta ba – Nuhu Abdullahi

Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood Nuhu Abdullahi wanda aka fi sani da Mahmoud, ya bayyana cewa a ɗan tsakanin nan irin nasarorin da ya samu bai taɓa tunanin zai same su ko a mafarki ba.

Jarumi Nuhu Abdullahi ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba da ta gabata ne a shafinsa na facebook cikin wata gajeruwar nasiha da ya yiwa matasa akan kaucewa miyagun dabi’u da kuma fita daga dukkanin wata sabga da za ta bata musu lokaci.

“Salam, kirana ga ƴan uwana matasa mu mai da hankali wurin ciyar da kan mu da wasunmu gaba mu daina ɓata lokaci akan abinda zai ɓata mana lokaci wanda bai da amfani”

Ya ƙara da cewa ” A ƴan shekaruna na samu cigaban da ko a mafarki ban yi zaton zan samu ba, amma Allah cikin ikon sa ya sa na samu. Mu zama masu jajircewa akan abinda ya ke gaskiya da kuma amana mu kuma guji ƙarya da sharri da hassada da ƙyashi, Allah sai ya taimake mu, wanda ya yi min wancan ƙaryar na yafe masa, kuma Allah ya shiryar da shi. Amin”. In ji Nuhu Abdullahi

Wannan gajeruwar nasihar da Tauraron Kanywood ɗin tana a matsayin martani ga wani mai suna Ishaƙa Usman Wali da ya rubutawa jarumin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya ke ikirarin daukakar da Nuhu Abdullahin ya samu ta sa ya manta da asalinsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet