Connect with us

Labarai

Gwamnatin Ganduje za ta gina banɗakuna 58 a faɗin jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta gina banɗakuna 58, tare da gyara wasu masu tarin yawa da suka lalace a wani ɓangare na bikin ranar yaƙi da bahaya a sarari.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya baiyana hakan a tashar mota ta Kano Line yayin gangamin wayar da kan al’umma game da illar bahaya a sarari.

Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware ranar 19 ga watan Nuwamban kowacce shekara matsayin ranar yaƙi da bahaya a sarai.

Dakta Getso, wanda Babban Sakataren maaikatar, Adamu Abdu Faragai ya wakilta, ya ce taron ya mayar da hankali wajen wayar da kan alumma musamman direbobi da matafiya a kan illar bahaya a sarari da kuma yadda zaa kawo karshen matsalar.

Ya ce “yau mun haɗa hannu da shugabannin tashar mota ta Kano Line domin wayar da kan al’umma game da illar yin bahaya a sarari, musamman guraren kasuwanci da taruwar alumma”.

“Idan zaa iya tunawa a ranar 19 ga watan Yunin 2021 da muke ciki zababban gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da gangamin yaki da bahaya a fili inda ya umarci maaikatar Samar da ruwan sha da maaikatar Muhalli da su yi aiki tare domin yaki da matsalar”.

Adamu Faragai ya ce gwamnatin jihar Kano ta a samar da gurare 58 domin gina sabbin bandakuna tare da gyara wadanda suka lalace Wanda zasu zama Kari akan guraren bahaya sama da 400 da ake dasu a cikin kwaryar birnin Kano.

Ya ce “dukkan matakan da zamu dauka da hanyoyin da zamu bi, za muyi kokarin binsu wajen ganin an gani sabbin bandakuna domin cigaban alumma”.

A baya-bayan ne asasun tallafawa Yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ta ayyana kananan hukumomi jihar Kano 10 Wanda baa samun rahotanni bahaya a fili Wanda kananan hukumomin sun hada da Sumaila da Wudil da Garko da Gaya da Dawakin Tofa da Doguwa da Takai da Madobo da Danbatta da kuma Kabo.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet