Featured
Darasin da ya kamata mu ɗauka daga rayuwar ɗan ƙwallon ƙafa Francis Joseph Coquelin
Wata rana wani yaro mai suna Francis haifaffe kuma mazaunin kasar Faransa ya shiga ajinsu na makaranta ya zauna. Babu jimawa sai malamarsu tazo aka fara darasi. Da fara darasin sai malamar tasu tayi wa Francis tambaya wadda ya kasa bada amsarta. Sai tayi dariya tace masa: “wannan yaro mugun daƙiƙi ne, sai dai kayi tallan jarida a bakin titi idan ka girma”. Wannan jawabi na malama ya sosa ran Francis. Amma sai yayi shiru bai ce ƙala ba.
Shekaru goma sha biyu da yin wannan tattaunawa wannan yaro Francis ya zamo ɗaya daga cikin ƴan wasa sha ɗaya da zasu wakilci ƙungiyar Arsenal a gasar firimiyar Ingila a filin wasa na Old Trafford. Bayan shekara ɗaya kuma ya zamo ɗaya daga gwaraza wanda ƙungiyar ta dogara dasu. Masu kallon ƙwallo sunfi saninsa da Francis Coquelin, wanda Henry yayi wa laƙabi da ɗan sanda, saboda iya tsaron tsakiyar fili.
Bayan Arsenal taci gasar FA Cup a shekarar 2015 ne dai aka yi hira da shi, inda ya ce: “ina ma zan sake ganin wannan malama tawa, da nayi mata alherin da albashin masu basira ba zai iya bata ba. Zan tuna mata cewa uwar data haifeni bata haifi daƙiƙi ba, don kuwa gashi yau ina bugawa Arsenal wasa”. Yayi wannan batu yayin da yake zubda ƙwalla, alamar har a sannan zancen yana yi masa ciwo.
Sai ɗan jaridar ya tambaye shi: “Shin wannan maganar tata ta yi maka wani tasiri ne?” Sai Francis yace: “Ko rauni naji, idan na tuna maganar, sai naji na ƙagu na samu lafiya na dawo filin wasa”.
Coquelin dai haka ya zamo gwarzo wanda ya lashe gasar FA da CS guda uku-uku a ƙungiyar Arsenal. Bayan Wenger ya tafi sai ya koma Valencia inda ya lashe gasar Copa Del Rey a hannun shugaban masu wasan atisayen da ba’a taɓa kamar sa ba a tarihin ɗan Adam – Lionel Messi. Bayan shekaru biyu ya koma Villarreal inda ya taimakawa ƙungiyar ta ci kofi na farko a tarihin ta – wato Europa League a hannun Anti mai jan lesi ta ƙasar Ingila – Manchester United. Kuma har yanzu yana nan yana taka leda cikin nishaɗi da gogewa!
Wannan labari na Francis babban ƙalubale ne ga malaman aji. Mafi akasarinsu sunfi nuna kulawa ga dalibai masu saurin ganewa. Kuma sun nuna karamci gare su. Su kuma marasa ganewa da wuri suna binsu da magana maras daɗi. Abin mamakin shi ne ɗalibi yana iya manta kowanne irin karatu, amma banda kalmar yabo ko suka da malaminsa ya taɓa fada masa. Hakan ya sanya dole malamai su yi taka tsantsan da ɗalibai, musamman yara masu ƙananan shekaru.
Musamman mu a gida Nijeriya. Ɗan abinda zai sa goben yaro ta lalace bai kai ya kawo ba. Da mutum ya rasa ƙwarin gwiwarsa shi ke nan komai ya lalace. Shi ya sa kalmar ƙwarin gwiwa ya da ce ta zamo wajibi a tsakanin masu son ganin goben ƙasarmu ta yi kyau. Da fatan zamu lura!
M.A Iliasu
