Labarai
Rikicin APC A Kano: Jam’iyyar APC a Kano ta Ganduje ce da Ɗan Sarki – Fa’izu Alfindiki
Shugaban ƙaramar hukumar birnin Kano, Fa’izu Alfindiki, ya bayyana cewa jami’yyar APC mallakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce fa Abdullahi Abbas Sanusi, saboda haka dole kowanne ɗan jam’iyyar ya zama mai bin umarnin Gwamnan da kuma shugabancin Abdullahi Abbas ɗin.
Fa’izu Alfindiki wanda ya yi fice wajen bayyana ra’ayinsa tare da kare muradan gwamna Abdullahi Umar Ganduje da jam’iyyar APC a shafin Facebook, ya yi wannan furucin ne jim da wata babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin da bai yiwa tsagin gwamnati daɗi ba.
“Da an ƙi da an so kwalba uwar turare jam’iyya ta Ganduje ce da Ɗan Sarki @Kano Sai Ganduje”
Haka kuma shugaban ƙaramar hukumar ta Birnin Kano ya ƙara da cewa tabbas lokacin gwagwarmayar siyasa ta zo kuma za su fafata da dukkanin wanda ya shata layi da su.
“Kura uwar kare, an buga gangar ranar kuma ta buɗe. Lokacin kuma yayi Allah ya ba mu sa’a da rabo.@Kano sai Ganduje”.
Hakazalika Fa’izu Alfindiki din ya ce tsagin da su ke jayayya da shugabancin Abdullahi Abbas su saurari irin matakin da za su dauka akan wannan al’amari.
“Wasa farin girki. Ƙarya fure take ba ta ƴaƴa yaro bari murna karen ka ya kama zaki. Da mu ku ke zancen ku jiraye mu”
Idan za a iya tunawa dai a jiya Talata ne wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam’iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da aka yi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar da ma dukkan shugabannin da bangaren Ganduje ya gudanar.
