Featured
Buhari ya nemi ƴan Najeriya su yi addu’a ga Amurkawan da guguwa ta yi sanadin mutuwar su
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Amurka da mutanen ƙasar kan mahaukaciyar guguwar da ta kashe sama da mutum 100 a jihohi shida.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce ya damu ƙwarai kan yadda gidaje da makarantu da wuraren sana’o’i da asibitoci suka lalace.
Shugaban ya yi kira ga mutanen Najeriya su taya sauran mutanen duniya addu’a ga waɗanda suka rasa ransu da kuma samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Sama da mutum 100 ne dai suka rasa rayukansu a guguwar wadda ta fi ɓarna a jihar Kentucky ta Amurka.
