Labarai
Gwamnatin Kano ta ragewa ƴan adaidaita-sahu kuɗin sabunta rijista zuwa ₦5,000
Hukumar kula Da Tituna da Sufuri ta Jihar Kano, KAROTA ta cimma matsaya tsakaninta da matuƙa babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da adaidaita-sahu kan biyan kuɗin sabunta rijista na shekara-shekara.
A makon da ya gabata ne dai dubban matuƙa adaidaita-sahun su ka tafi yajin aiki domin nuna rashin amincewarsu da N8,000 kuɗin sabunta rijistar da KAROTA ta ce su riƙa yi shekara-shekara.
Da ga bisani ne sai matuƙa baburan su ka zauna da gwamnatin da wasu masu ruwa da tsaki, in da a ka shawo kan lamarin.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jamaa na KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya sanyawa hanu a yau Laraba, hukumar ta ce an cimma matsaya za su riƙa biyan N5,000 kudin rijistar, maimakon N8,000 da a ka sanya da farko.
Sanarwar ta ce an yi zaman yarjejeniyar ne a Sakateriyar Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, reshen Jihar Kano.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa, an shafe fiye da awanni 4 a na tattaunawa da ɓangarori biyun, in da Barista Abba Hikima Fagge ya wakilci ƴan adaidaita-sahu, shi kuma Shugaban KAROTA, l Baffa Babba Dan’agundi da kuma Gamayyar Halastattun ‘Yan Ƙungiyoyin Adaidaita-Sahu na Jihar Kano.
A zaman, in ji sanarwar, an amince da ragewa ƴan adaidaita-sahun biyan kuɗin shaidar tuƙi sabo daga ₦18,000 zuwa ₦12,000, in da sabunta wa kuma ya zama daga ₦8,000 zuwa ₦5,000.
Zaman ya amince da biyan harajin kulum-kullum na N100, har da ranar Lahadi, wanda a baya sai dai su biya kuɗin ranar Lahadi ɗin a ranar Litinin.
Haka kuma zaman ya amince cewa kowanne ɗanan adaidaita-sahu ya biya wannan kuɗi nan da ƙarshen watan Febrairu na wannan shekarar, in da a ka ce ƙin biyan kuɗin a wannan lokacin zai sai a biya kuɗin baya kamar yadda zaman ya amince.
An gudanar da zaman ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Jihar Kano, Barista Aminu Sani Gadanya.
Da ya ke jawabin a wajen tattaunawar, Dan’agundi ya yabawa Shugaban Rundunar tsaro ta farin kaya, wanda bisa ga gudummawar da ya bayar ne a ka samu wannan matsaya.
Sannan ya bayar da tabbacin cewa KAROTA da matuƙa adaidaita-sahu sun samu kyakkyawar fahimtar juna a lokacin da su ke gudanar da tuƙi a kan titi.
