Connect with us

Labarai

Ƴan fashin dajin da su ka sace ɗaliban FGC Yauri sun aure mata 13 daga cikin ɗaliban

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya bayyana cewa ƴan bindigar da su ka sace ɗaliban makarantar sakandiren Tarayya ta Yawuri a jihar Kebbi, sun auri ƴan mata 13 daga cikin ɗaliban, inda wasu daga cikinsu ma har sun samu juna biyu.

Rahoton kuma ya bayyana cewa tsakanin 11 zuwa 14 daga cikin ɗaliban har yanzu suna hannun Dogo Giden, kuma namiji ɗaya ne kawai a cikinsu.
Ranar 16 ga watan Yunin shekarar 2021 ne dai ‘yan bindigar suka sace wadannan dalibai daga makarantarsu, inda suka kwashe su, su sama da 100 da wasu malamansu, suka tafi da su daji.
Haka kuma gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya lashi takobin ƙwato yaran tun lokacin da aka sace su, sai dai har zuwa wannan lokaci babu labarinsu, ko ma na irin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na kubutar da su.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro bayan sace daliban, gwamnan ya ce “za mu shiga daji mu kwato su, dama abun da aka rantsar da mu mu yi kenan, don haka duk wanda ke ganin zai dauki yaranmu muna da rai ya yi karya.

Hare-haren tare da satar daliban sun biyo bayan wanda wani kasurgumin dan bindiga mai suna Auwal Daudawa ya fara jagoranta a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara a Jihar Katsina a watan Disambar 2020, inda suka sace dalibai sama da 200.

Satar mutane don neman kudin fansa musamman dalibai, matsala ce da ta zama ruwan dare a fadin Najeriya a shekarun baya-bayan nan, sai dai mahukunta na cewa suna yin iya bakin kokarinsu don shawo kan matsalar, amma kuma kusan matsalar sai Karuwa take yi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet