Labarai
Matsalar Tsaro: Ƴan fashin daji sun hallaka DPO da ƴan sanda biyu a Neja
Wasu rahotanni daga jihar Neja da ke fama da matsalar tsaro sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga sun yi wa ofishin ƴan sanda a Nasko ƙofar rago tare da hallaka baturen ƴan sandan yankin (DPO).
An kashe DPO Umar Mohammed Digari a ranar Talata da wasu ƴan sanda biyu, kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar cewa ƴan bindigar sun kai harin ramuwar gayya ne bayan harin da aka kai masu a maɓuyarsu inda aka ƙwace shanun da suka sato sama da 800.
Sai dai babu wata sanarwa daga rundunar ƴan sandan jihar da ta tabbatar da lamarin.
