Siyasa
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta kori ƙarar da Ɗan zago ya shigar kan shugabancin Abdullahi Abbas
Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a A. M. Liman, ta kori ƙarar da Alhaji Ahmadu Haruna Ɗan Zago ya shigar a gabanta ta ƙalubalantar shugabancin Abdullahi Abbas na jam’iyyar APC a Kano.
Kotun ta yanke hukuncin ne a zamanta na yau Talata.
Yayin bayyana hukuncin, alƙalin ya ce, ya kori ƙarar kasancewar ne saboda a cikin ƙunshin ƙarar ba a sanya hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ba.
A zantawarsa da manema labarai, lauyan Abdullahi Abbas Barista Marcellunus Duru, ya ce, tun a baya, ya sanar da kotun cewa ba ta da hurumin sauraron shari’ar.
Haka shi ma lauyan Ɗan Zago Barista Rabi’u Sa’id Rijiyar Lemo ya bayyana cewa ƙorafin wanda yake karewa bai danganci hukumar INEC ba ne, kawai suna ƙorafin ne a kan rashin cika sharuɗan Abdullahi Abbas na zama shugaba.
Freedom Radio ta ruwaito cewa lauyan na mai ƙara ya ce, Abdullahi Abbas bai sauka daga muƙaminsa ba har lokaci ya ƙure.
Haka kuma ya ce, “Za mu nazarci hukuncin kotun domin yin shirin ɗaukar mataki na gaba”.
