Labarai
Borno: Ƴan sanda sun cafke mutum 8 bisa zarginsu da yin garkuwa da mutane
Rundunar ƴan sanda jihar Borno, ta ce jami’anta sun cafke mutum 8 bisa zarginsu da yin garkuwa da mutane.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Abdu Umar, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a Larabar nan.
Ya ce rundunan cafke waɗanda ta ke zargin ne daga watan Maris zuwa Afirilun da ya gabata.
Haka kuma ya ƙara da cewa yawancin waɗanda suka kama ana zargin su da hannu wajen garkuwa da mutane a Mubi da ke Adamawa, Taraba da kuma ita jihar ta Barno.
