Labarai
Ƙungiyar NLC ta soki lamiri gwamna Ganduje na ciyo bashin biliyan 10
Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC shiyyar Kano, ta soki lamirin gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na ciyo bashin naira biliyan 10 domin sayen kyamarorin na CCTV.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke sa hannu shugaban kungiyar Kwamared Kabiru Ado Minjibir da sakatarenta Hussaini Budah wadda suka fitar Juma’a.
A cewar NLC za a ciyo bashin ne a dai-dai lokacin da ma’aikata ke cikin halin ƙuncin rayuwa, kuma gwamnatin ta gaza sauke haƙƙin tsaffin ma’aikata da suke bi ta bashin kuɗaɗe Garatuti da fansho da suka haura Naira biliyan 27.
Haka kuma ƙungiyar ta ce, ba za ta lamunci a ciyo bashin maƙudan kuɗin ba wai don a sanya CCTV kawai.
Ƙungiyar ta NLC ta kuma ce tsaro abu ne mai matuƙar muhimmanci, amma dai ba sai an ciyo wannan bashi mai yawa za a daƙile shi ba, maimakon hakan gwara a ciyo bashin don biyan haƙƙin tsofaffin ma’aikata.
