Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Shugaba Buhari ya aike wa majalisa sunayen Mutanen da zai naɗa ministoci
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya gabatar wa majalisar dattawa sunayen mutanen da ya zaɓa domin zama ministoci.
Shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawan, ne ya karanto sunayen nasu a zaman majalisar na yau Talata.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa waɗanda shugaba Buhari ya aike da sunayen nasu sun haɗa da Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano da Umana Okon Umana daga Akwa Ibom da Henry Ikechukwu Iko daga jihar Abia.
Sauran sun haɗa da Ademola Adegoroye ɗan asalin jihar Ondo da kuma Odum Odi daga jihar Rivers da Goodluck Nnana Opia daga Imo da kuma Joseph Ukama daga jihar Ebonyi.
Haka kuma Sanata Ahmad Lawan ya ce, majalisar za ta tantance mutanen domin naɗa su a matsayin ministocin nan ba da jimawa ba.
