Labarai
Saƙon Sallah: Shugaba Buhari ya buƙaci ƴan Najeriya su sanya buƙatun ƙasa a gaba da komai
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya buƙaci ƴan Najeriya da su sanya buƙatun ƙasa a gaba da komai tare da yin riƙo addini domin samun haɗin kai a tsakanin ƴan kasa.
Hakan na cikin saƙon barka da Sallah ga Musulmi da mai taimaka wa shugaban na musamman kan harkokin yaɗa labarun Malam Garba Shehu ya fitar yau Asabar.
Sanarwar ta ce, Shugaba Buhari ya ce “Matuƙar mutane na amfani da koyarwar addini, to za a samu mafita kan yawancin matsalolin da ake fuskanta a yanzu.”
Haka kuma a cewar Shugaban ya kamata addini ya kasance a matsayin abun da za a yi amfani da shi wajen yin abu mai kyau.
Ya ƙara da cewa satar kuɗin ƙasa da wasu jami’an gwamnati ke yi, manuniya ce ta barin koyarwar addini.
Shugaba Buhari ta cikin sanarwar ya ƙara cewa ”Wasu mutanen a yanzu ba sa tsoron Allah, inda suke sanya abubuwa su zamanto masu wahala ga wasu”.
Haka kuma, shugaba Buhari A karshe ya taya Musulmin Najeriya da ma na duniya baki ɗaya murnar bikin Sallar layyar ta bana.
Haka kuma ya ce ”Wasu shugabannin na yin watsi da rantsuwar da suka yi yayin kama aiki ta hanyar karkatar da kuɗaɗen da aka tanada domin amfanar ƴan Najeriya i zuwa aljihunansu.
A batun matsalar tsaro da tsadar rayuwa kuwa da Najeriya ke fuskanta, shugaba Muhammadu Buhari, ya sha alwashin cewa ba zai gajiya ba har sai ya samar wa ƴan Najeriya mafita.
