Siyasa
Jam’iyyar APC ta ƙaddamar da Kashin Shattima a matsayin abokin takarar Tinubu
Jam’iyyar APC mai mulki da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu sun ƙaddamar da Sanata Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen baɗi.
Solacebase ta ruwaito cewa, An gudanar da bikin kaddamarwar ne a ɗakin taro na Shehu Musa Yar’adua da ke birnin tarayya Abuja, yau Laraba.
Haka kuma rahotonni sun bayyana cewa bikin ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na Najeriya Sanata Abdullahi Adamu da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum da gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da sauran ƙusoshin jam’iyyar ta APC.
