Lafiya
Da ɗumi-ɗumi: Shugaba Joe Biden ya kamu da cutar Corona
Labaran da ke fitowa daga fadar mulkin ƙasar Amurka White House a yanzu haka na bayyana cewa shugaban ƙasar Mista Joe Biden, ya kamu da cutar korona.
Fadar ta White House ta bayyana cewa an gano shugaban ya kamu ne sakamakon gwajin da aka yi masa wanda ya tabbatar da hakan.
Sai dai fadar mulkin ta ƙara da cewa, shugaban yana nuna wasu daga cikin ƙananan alamomin kamuwa da cutar.
