Kasuwanci
Kano: Hukumar CPC ta bankaɗo wurin da ake sayar wa manoma gurɓataccen Taki
Hukumar kare haƙƙin masu saya da masu sayar da kayayyaki ta jihar Kano jihar Kano CPC, ta bankaɗo wani wuri da ake ajiye gurbataccen takin zamani a garin Gunduwawa da ke yankin ƙaramar hukumar Gabasawa.
Shugaban hukumar Baffa Babba Dan’agundi, ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar, Malam Musbahu Yakasai yau Talata.
Ya ce, “Mun samu bayanan sirri ne kan inda aka shaida mana cewa akwai wani mai wurin adana takin zamani wanda ke cakuɗa shi da yashi kuma ya siyarwa manoma a matsayin mai kyau.”
Ya kuma ce, “Hakan yasa muka ɗauki matakin rufe wurin domin kare manoma daga amfani da takin maras kyau.
Malam Musbahu Yakasai, ya kuma buƙaci al’ummar jihar Kano, da su cigaba da bawa hukumar bayanan irin wadan nan gurare domin kare rayukan al-umma.
