Labarai
Shugaba Buhari ya buƙaci majalisar dattawa ta tabbatar da Olukayode Ariwoola a matsayin Alƙalin Alƙalai
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya buƙaci majalisar dattawa kan ta tabbatar da muƙaddashin Alƙalin Alƙalai Olukayode Ariwoola a matsayin Alkalin alƙalan Najeriya.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan,, ne ya karanta wasiƙar da shugaban ya aike wa majalisar yayin zamanta na yau Talata.
BBC ta ruwaito cewa Olukayode Ariwoola, shi ne muƙaddashin Alkalin Alkalai tun bayan da Alƙalin Alƙalai Ibrahim Tanko Muhammad ya ajiye aiki a kwanakin baya da ya ce, ya ajiye dalilin rashin lafiya.
