Labarai
Katsina: Ƴan bindiga sun sake kai hari Ƙauyen Dantsauni da ke Batagarawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta tabbatar da rahoton sake kai harin da ‘yan bindiga suka yi a ƙauyen Dantsauni da ke karamar hukumar Batagarawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Gambo Isah, ne ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai.
SP Gambo Isah, ya ce mutum guda ya rasu sannan mutane biyu sun jikkata sakamakon harin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ‘yan ta’addan dauke da manyan makamai ne suka kai harin kimanin kwanaki uku bayan kai makamancinsa a kauyukan Babbar Ruga da Kwarin Maikotso da kuma Kore, inda suka hallaka mutane biyu tare da sace mutum takwas.
Haka kuma ta ruwaito cewa yayin harin ‘yan bindigar na kauyen Dantsauni, bata garin sun yi awon gaba da mutane da dama da suka hada da mata da kananan yara.
