Connect with us

Featured

Abbas Yusha’u ya zama Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Sha’aban Sharaɗa

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADP, Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya amince da naɗin Abbas Yusha’u Yusuf a matsayin kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen sa.

Sha’aban Sharada ya bayyana amincewar ne a jiya Lahadi yayin ganawar sa da manema labarai a birnin Kano.

Ya ce ya amince da naɗin Abbas Yusha’u ne la’akari da irin gogewar da ya ke da ita a harkar aikin jarida tsawon lokaci.

Haka kuma ɗan takarar gwamnan ya buƙaci sabon kakakin da ya yi aikinsa bisa yadda doka ta tanadar da kuma kyautata hulɗa tsakaninsa da ƴan jaridu, domin hakan zai sa a samu kyakkyawan sakamako.

Abbas Yusha’u Yusuf shi ne sakataren ƙungiyar ƴan jaridu masu ayyukan su a shafukan intanet reshen jihar Kano, kuma mawallafin jaridar Nigerian Tracker.

Abbas, ya yi karatun digirinsa na farko da na biyu akan harkar aikin jarida da sadarwa a jami’ar Bayero ta Kano.

Hakazalika sabon Kakakin ya yi aiki a kafafen yaɗa labarai da su ka haɗar da gidan rediyon Rahama da Freedom da kuma rukunin gidajen rediyon Vision.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet