Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA ta sake cafke babbar mota maƙare da Barasa

Hukumar kula da Zirga-zirga ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta sake cafke babbar motar ɗaukar kaya wadda ke maƙare da Barasa.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jam’i’inta na yaɗa labarai Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar da yammacin yau Litinin.

Sanarwar ta ce, Jami’an hukumar ta KAROTA sun samu nasarar cafke motar, lokacin da direbanta ke yunƙurin shigowa cikin jihar Kano da misalin karfe 3:00 na dare.

Haka kuma ya ce, “An kama motar ne a kan titin zuwa Katsina kusa da kasuwar Dawanau lokacin da Direban motar ke yunƙurin shigowa cikin Kano bayan da ya canja hanyar da ya saba shigowa ta kan titin zuwa Zariya duba da yadda hukumar ta ƙara baza jami’anta a kan titin, hakan ta sa suka canja hanyar shigowa cikin Kano kamar yadda hukumar ta sami rahoton sirri.”

“Bayan da aka cafke motar ne sai Direban ya tsere tare da barin motar wadda take maƙare da Barasa a cikinta”, inji Nabulusi.

Haka kuma sanarwar ta ce, Shugaban hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya yaba da ƙoƙarin jami’an da suka sami nasarar cafke motar cikin tsakiyar dare.

“Hukumar ta KAROTA ta ce zata miƙa Giyar ga Hukumar Hizba domin ɗaukar mataki na gaba da zarar ta kammala bincike,” cewar sanarwar.

Ko a kwanakin baya hukumar ta KAROTA ta miƙa Manyan motoci guda biyu wanda ta kama ɗauke da Barasa ga Hukumar Hizba da yawanta ya kai Kwalba dubu Arba’in da biyar wadda kuɗinta ya haura naira miliyan Hamsin hamsin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet