Featured
Ƴan Jarida suna da daraja matuƙa a Najeriya – Gwamnan Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed Abdulkadir, ya ce ƴan jarida da sauran masu aikin yaɗa labarai sune mutanen da suka fi kowa daraja a Najeriya.
Mohammed, ya bayyana haka ne a Bauchi yayin da yake mika kyautar sabbin motoci kirar Toyota Hiace guda biyu ga Ƴan Jaridar gidan gwamnati da kuma kungiyar yan jarida ta kasa (wato NUJ) a jihar.
A cewarsa, masu aikin yaɗa labarai a ko da yaushe suna fama da takura da ƙalubalen tattara labarai Kuma duk da Irin gudunmawa da suke bayarwa ga al’umma amma ba su da albashi mai kyau.
Ya ƙara da cewa ƴan jarida suna shan wahala matuka duk da cewa sun fi kowa bada gudunmawa wajen ci gaban al’ummar Kasa.
Mohammed, wanda ya ce ya bayar da motocin ne domin nuna cewa aikin jarida da ƴan jarida na da mutunci, ya ƙara da cewa dole ne a mutunta su tare da karfafa musu gwiwa su yi aiki yadda ya kamata don samar da yanayi mai kyau.
Ya ce idan aka yi la’akari da ayyukan su, dole ne a ba wa ƴan jarida daraja ta fuskar gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.
Ya ce hakan zai sa aikin ya kasance mai daraja ta yadda ƴan jaridar za su samu albashi da alawus-alawus da sauran abubuwan more rayuwa.
Daga ƙarshe ya jaddada alƙawarin sake gyara sakatariyar ƙungiyar NUJ a jihar kafin cikar wa’adin mulkin sa.
