Labarai
Hukumar NAPTIP ta cafke fiye da mutane 500 da za a tura su ci rani ƙasashen ƙetare
Hukumar yaƙi safarar bil -Adama ta Najeriya NAPTIP, ta kama wasu mutane su fiye da ɗari biyar wadanda aka shirya tura su wasu ƙasashen ƙetare a bana.
Shugaban hukumar shiyyar Kano Abdullahi Babale, ne ya bayyana hakan ga manema labarai da yammacin Talatar makonnan.
Ya ce, tun farko hukumar ta NAPTIP, ta samu nasarar kame wasu ƴan ƙasar Ghana da Kamaru ne su uku, bisa zargin su da laifin safarar mutane zuwa ƙasashen ƙetare.
Haka kuma shugaban ya ƙara da cewa yanzu haka irin wannan mummunar ɗabi’a ta safarar mutane na ƙara yin ƙamari a jihohin Kano da Jigawa da Katsina da Kaduna da kuma jihar Bauchi.
Abdullahi Babale, ya ƙara da cewa, waɗanda ake zargin suna yin safarar mutanen ne zuwa ƙasashen ƙetare ne domin yin aikatau da karuwanci har ma da aikata wasu manyan laifuka.
Haka kuma ya ƙara da cewa, ya kamata gwamnatoci su riƙa gudanar da tarukan wayar da kai ga al’umma domin faɗakar da su irin illolin da irin wannan ci-rani ke tattare da shi.
