Ilimi
Hukumar WAEC ta bayyana dalilan riƙe sakamakon wasu ɗalibai
Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun Sakandare ta yammacin Afirka WAEC, ta bayyana dalilan riƙe sakamakon wasu ɗalibai na jarrabawar.
Shugaban hukumar Mista Patrick Areghan, a zantawarsa da manema labarai ya ce, Hukumar ta riƙe sakamakon ɗaliban ne bisa zargin su da satar amsa.
Haka kuma ya ƙara da cewa, Hukumar za ta saki sakamakon ɗaliban da ba su da laifi da zarar ta kammala bincike.
Hakan dai ta biyo bayan yaɗa jita-jitar cewa hukumar ta rike sakamakon wasu dalibai ba tare da bayyana dalilai ba.
