Labarai
Kotu ta yanke wa Evans hukuncin ɗaurin shekaru 21
Kotun sauraren ƙararrakin aikata manyan laifuka da ke Ikeja a jihar Lagos, ta yanke hukuncin daurin shekaru 21 ga kasurgumin mai garkuwa da mutanen nan Chukwudumeme Onwuamadike da aka fi sani da Evans tare da abokin ta’asarsa Victor Aduba bisa samun su da kaifin yin garkuwa da wani mutum Sylvanus Ahanonu Hafia.
Kotun ƙarkashin jagorancin mai shari’a Oluwatoyin Taiwo, ya yanke hukuncin ne a zamanta na yau Litinin bayan da ta sam su da hannun dumu-dumu wajen yin haɗin baki da kuma yin garkuwa da Sylvanus Ahanonu Hafia da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar 23 ga watan Yunin shekarar 2014.
Kotun ta kara da cewa wadanda aka tuhuma din sun sace mutumin ne akan titin Amuwo Odofin da ke jihar ta Lagos tare da bukatar kudin fansa har Dalar Amurka Milyan biyu.
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo, ya ƙara da cewa, wannan hukunci zai zama izina ga sauran masu garkuwa da mutane da ke faɗin Najeriya.
