Labarai
Jigawa: UNICEF ya tallafa wa waɗanda ambaliya ta shafa da Naira miliyan 230,700
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ya bayar da gudummawar tallafin Naira miliyan 230 da dubu 700 ga gwamnatin Jihar Jigawa domin rabawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Shugabar ofishin UNICEF na Kano Rahama Farah ce, ta bayyana hakan lokacin da ta gabatar da tallafin ga mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Umar Namadi.
Farah wadda babban jami’in sashen harkokin Ilimi na UNICEF, Michael Banda ya wakilta, ya ce matakin ya biyo bayan tantance ƴan gudun hijira, a sansanonin da ƴan gudun hijirar da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙananan hukumomin jihar ke fakewa.
Ƙafar Daily News 24,ta ruwaito cewa, tallafin ya kasance a fannonin Ilimi da abinci da Ruwan sha da tsaftar muhalli da sauransu.
A cewarsa, “Muna godiya ga Mataimakin Gwamnan bisa karɓar tawagar mu a ziyarar da ta kai a baya, sannan kuma damar da aka ba wa UNICEF, gwamnati da sauran abokan hulɗa, sun gudanar da aikin tantance matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa.”
