Connect with us

Labarai

Kaduna: EFCC ta Cafke mutane 9 bisa zargin su da safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA, shiyyar jihar Kaduna, ta kama wasu mutane tara bisa  zargin su da safarar miyagun ƙwayoyi.

Kwamandan hukumar Umar Adoro, ne ya bayyana hakan da safiyar yau Talata a Ganawarsa da manema labarai.

Ya ce, an kama waɗanda ake zargin ne a wurare daban-daban na jihar a tsakanin ranar 6 zuwa 16 ga wannan watan da muke ciki na Oktoba.

Umar Adoro ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ne a unguwar Talabijin da ke Kaduna inda kuma aka same shi da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 26, yayin da wani da ake zargin kuma aka cafke shi a birnin Zariya shi ma da Wiwi mai nauyin kilogiram 15.5.

Kwamandan ya ce an kama wasu waɗanda ake zargin a yankunan Kakau da Gonin gora da Tashar Yari da kuma biyu daga yankin Jos ɗin jihar Filato.

Haka kuma shugaban na NDLEA, Ya ce, an kuma gano sinadarin Methamphetamine mai nauyin Kilogiram 192.2 da kuma Naira 300,000 na bogi daga hannun biyu daga cikin waɗanda ake zargin.

Umar Adoro, ya kuma ce, an kama wani da ake zargi a ranar 16 ga Oktoba, inda aka same shi da allunan Tramadol 919 masu nauyin giram 400 da kuma alluran Diazepam 5,000 masu nauyin giram 900 da kuma allunan Exol-5 25,000 masu nauyin Kilogiram 8.2.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet