Connect with us

Labarai

Tinubu- Zan ɗora a kan irin kyawawan manufofin shugaba Buhari

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen baɗi  Bola Ahmed Tinubu, ya ce, idan ya karɓi mulkin Najeriya zai ɗora ne a kan salon jagorancin mulki irin na shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Bola Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mahalarta taron duba ayyukan ministoci karo na uku a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja jiya Talata.

Haka kuma,ya ce, gwamnatinsa za ta duƙufa wajen cigaba da ayyukan Buhari; musamman ayyukan da ya gada da nufin samar da wadata ga ƴan kasa.

Ya kara da cewa manufofin na sa za su ta’allaka ne ga samar da kyakkyawan tsarin gudanar da mulki da gyara al’ummar kasa.

Tinubu, ya kuma ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ƙoƙari wajen magance tashe-tashen hankula ya yi wa Boko Haram illa sosai tare da shawo kan lamarin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet