Siyasa
Zan shiga Muhawarar da kamfanin Media Trust ya shirya- Ɗan takarar gwamna a PRP
Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar PRP Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana aniyarsa ta shiga muhawarar da kamfanin Media Trust Limited mamallakin kamfanin jaridar Daily Trust da Aminiya da tashar Trust TV zai shirya wa ƴan takarar gwamna.
Salihu Tanko Yakasai ya ba da wannan tabbacin ne lokacin da shugaban kwamitin tsara muhawarar Dakta Suleiman A. Suleiman da mambobin kwamitin suka kai masa ziyara a ofishinsa.
Sanarwar da mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar PRP Suhaib Auwal Gwagwarwa ya fitar, ta ce Yakasai ba wai yana tabbatar da shiga ne kawai ba, har ma da gudanar abubuwan da za su bai wa sauran ƴan takara mamaki da ganin an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara saboda tsarin da shi da jam’iyyarsa suka yi wa al’ummar jihar Kano.
A cewar Salihu Tanko Yakasai, “Da alama zaɓen baɗi na ɗaukar wani salo na daban domin muna da gidan talabijin na Trust da ke tafka muhawara har ma da ƴan takarar gwamna da sauran kungiyoyi da su ma suke ƙoƙarin ganin an yi yakin neman zaɓe yadda ya dace.
“Wannan abun farin ciki ne, muna da shiri, kuma muna kan aiki kuma ina ba ku tabbacin cewa duk da cewa muhawarar ta rage watanni, ni ne zan yi nasara,” inji shi.
Muhawarar mai taken ‘Trust Nigeria 2023 Elections Debate’, ana sa ran za ta bai wa jam’iyyun siyasa da ƴan takararsu a babban zaɓe mai zuwa damar isar da tsare-tsare da ajandarsu ga masu kaɗa ƙuri’a.
