Uncategorized
Messi zai je Gasar Cin Kofin Duniya karo na biyar a tarihi
Lionel Messi zai ja ragamar tawagar Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar, kuma karo na biyar a jere da zai wakilci kasar.
Mai taka leda a Paris St Germain wanda shi ne kyaftin din tawagar, yana cikin jerin ‘yan wasa na Premier League biyar da za su wakilci Argentina.
Kociya, Lionel Scaloni ya hada ‘yan wasan da ke da kwarewa kamar Messi mai shekara 35 da Angel di Maria mai shekara 34 da matasa, ciki har da mai taka leda a Manchester City, Julian Alvarez.
Messi wanda ya fara buga Gasar Cin Kofin Duniya a Jamus a 2006 ya je ta Afirka ta Kudu a 2010 ya kuma halarci ta Brazil a 2014 da wadda aka yi a Rasha a 2018.
